Friday, November 1, 2019
Yadda Jarumi Ali Nuhu Ya Samu Karramawa A Kasar Indiya

Home Yadda Jarumi Ali Nuhu Ya Samu Karramawa A Kasar Indiya

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
A makon da ya gabata ne dai Jarumin masana'antar Fim ta Kannywood wato Ali Nuhu ya samu karramawa a kasar Indiya.

Ya samu karramawar ne daga wadansu dalibai 'yan Arewacin Nigeria da kuma malaman su Indiyawa a kasar ta Indiya bayan sun gayyace shi wani taron Al'adu

Daliban na karanta fannoni daban-daban kama daga fannin likita zuwa hada magunguna da injiniya da sauransu,” in ji Ali Nuhu kamar yadda ya shaida wa BBC. Jarumin ya ce baya ga wadannan dalibai, wasu makarantu a kasar sun ba shi lambobin yabo.

KARANTA WANNAN. Juruman 'Yan Mata 6 Mafiya Shahara A Kannywood

Ali Nuhu ya ce “Akwai makarantar Dayananda Sagar School of Physiotherapy su ma sun ba ni lambar yabo kuma sun nuna jin dadinsu kan yadda daliban Najeriya ke mayar da hankali kan karatunsu.”

Jarumin ya ce ya yi matukar farin ciki da wannan karramawa da kuma yadda malaman wadannan makarantu ke da sha’awar al’adun Hausawa. “Wadansu daga cikin malaman har fina-finan Hausa suke kallo saboda su ga yadda yanayin rayuwar Bahaushe take.

“Shi ya sa idan wani dan wasa ya zo taro irin wannan sukan karrama shi,” inji Ali Nuhu.


Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.