Thursday, November 21, 2019
RUKAYYA DAWAYYA A YANZU BANI DA SAURAYI A KANNYWOOD

Home RUKAYYA DAWAYYA A YANZU BANI DA SAURAYI A KANNYWOOD
Ku Tura A Social Media
A YANZU BANI DA SAURAYI a Kannywood cewar rukayya dawayya
Cikin shirin daga bakin mai ita da #BBC HAUSA suka kaddamar a yau sun yi hira ne da shahararriyar jaruma a masana'antar Kannywood wacce taga jiya taga yau wato Rukayya Umar wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya.

Ga kadan daga cikin tambayoyin da aka yi mata da kuma amsoshin da ta bayar,


1 Wanene saurayin ki a Kannywood?

Rukayya. "A yanzu bani da saurayi a Kannywood"

2 Da wa koka taba yin soyayya a Kannywood?

Rukayya. "Misbahu Ahmad"

3 Wanene saurayinki na farko?

Rukayya. Kasancewar ba a Nigeria na girma ba na girma ne a kasar Saudiyya saurayi na na farko wani balarabe ne sunan sa Faisal".

4 Yaushe zaki sake aure?

Rukayya. Nan ba da dade wa ba"

5 Me kike fara yi idan kika tashi daga barci?

Rukayya. Kasancewar gidana hana da fadi nakan fito na zagaya ina duba filawowi sai na zauna na yi ta Azkar"

6 Yaruka nawa kika iya magana da su?

Rukayya. Yaruka 3 Hausa Larabci Fulatanci English.

Zamu dakata a nan sai wani lokaci na gaba.

Kuci gaba da bibiyar zaurenhausa a ko da yaushe.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.