Sunday, November 24, 2019
RIKICI A KANNYWOOD LAIFIN NI DA ALI NUHU NE ADAM A ZANGO

Home RIKICI A KANNYWOOD LAIFIN NI DA ALI NUHU NE ADAM A ZANGO
Ku Tura A Social Media
Shahararren jarumi a masana'antar Fim ta Kannywood Adamu Abdullahi Zango wato (Adam A Zango) ya ce yaran sa da yaran Ali Nuhu sune ke haifar da matsala da rashin jituwa a Kannywood din.

Jarumi Adamu Zango ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Radio France International wato RFI.


Cikin wata tattaunawa da jarumin yayi da gidan Radio France International (RFI) ya bayyana cewa rikici da matsalolin da yaran sa dana fitaccen jarumi Ali Nuhu ke haifarwa a Kannywood ba laifin kowa ba ne sai shi da jarumi Ali Nuhu.

A cewar Adamu Zango da ace suna tsawatarwa ga yaran nasu to da zasu iya dakatar da su daga yin duk wani abu da zai haifar da rikici a masana’antar.

Jarumi Adam Zango ya kara da cewa ta bangarensa bai yadda yaransa su ci zarafin wani jarumi ba.

Idan zaku iya tunawa dai a watannin baya ne wani rikici ya kunno kai tsakanin manyan jaruman guda biyu wanda har sai da ta kai ga anje kotu, inda daga bisani kuma aka samu yin sulhu a tsakanin su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.