Saturday, November 23, 2019
DAFA SHAYI NE GADO NA BA WAKA BA ADO GWANJA

Home DAFA SHAYI NE GADO NA BA WAKA BA ADO GWANJA
Ku Tura A Social Media
Jarumi a masana'antar Fim ta Kannywood kuma shahararren mawakin Hausa Ado Isa Gwanja ya ce ko kusa shi ba dan daudu ba ne.

Silar fitowa ta a matsayin dan daudu a Fim shi ne akwai wani Fim da aka bukaci dan daudu ciki aka nemi 'yan daudu jar su 50 cikin su aka rasa wanda zai iya shi ne sai aka ce bara to a gwada dan masana'antar ana gwadani kuwa na yi dace da wurin,

Wannan shi ne farkon fara fitowa ta a dan daudu inji Ado Gwanja,

Farko dai Ado Gwanja ya fara ne da rera wakoki kasancewar bai samu karbuwa ba sai ya juya akalar sa zuwa fito wa a Fim

Wakokin Gwanja dai sun fi karbuwa ne wajen mata kamar yadda zaka ji a mafiya yawan wakokin sa mata yafi ambata ymawakin ya ce yana yin haka ne sabo da su mata sun fi son biki ma'abota nishadi ne
To wa zan ambata idan ba mata ba?" A cewar sa.

Gwanja ya musanta zargin da ake yi masa cewa yana furta kalmomin batsa cikin wakokin sa a inda yace To ni dai da Hausa nake waka kuma bahaushe yana da fahimta a iya sani na a duk wakoki na ba abun da ya shafi batsa ko kusa,


Matashin ya fara waka ne kusan shekaru 10 da suka gabata
Ra'ayi ne ya sa na fara waka" a cewar sa.

Ya kara da cewa shi ba gadon waka yayi ba shige yayi sai Allah ya bashi baiwa har ya samu karbuwar da yake kai a halin yanzu,

Yace idan gado ne da dafa shayi zan gada domin shi ne sana'ar mahaifi na a Kano"Kamar yadda yake a bayyane cewa mafi yawan jarumai ko mawaka na cin karo da matsaloli, sai dai Gwanja ya ce duk wanda ya samu kansa a matsala "to shi ya ga dama ya shige ta."
Kazalika mawakin ya ce shi a saninsa ba shi da wasu makiya ko abokan adawa a wannan harka, idan ma kuma akwai su to bai san da su ba. "Kazantar da ba ka gani ba kuma tsafta ce," in ji shi.


Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.