Sunday, October 6, 2019
Yadda zaka tsare WhatsApp din ka daga masu kutse

Home Yadda zaka tsare WhatsApp din ka daga masu kutse

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Masu bibiyar ZaurenHausa barkan mu da wannan lokaci
A yau zamu yi bayani ne game da yadda zaku tsare akawun din ku na WhatsApp daga sharrin masu kutse.


A yanzu halin da ake ciki wadansu bata garin mutane sun fito da wani salo na kwace wa mutane WhatsApp din su ba tare da sun sani ba,

Wadannan bata garin mutane zasu iya hawa WhatsApp din ka a duk lokacin da suka ga dama ba tare da ka sani ba a inda zasu iya amfani da wannan dama wajen aiwatar da duk abun da suke bukata ko dai su damfari wadansu ko wani abu daban,

Wannan dalili ne yasa muka zo muku da hanyar da zaku bi domin tsare naku akawun din daga sharrin su

Ku biyo ni


Farko idan ka bude WhatsApp application din ka ka duba can sama hannun dama sai Ku danna wannan digo 3 kamar yadda yake a wannan hoto dake kasaBayan kun danna zai baku option ciki har da Setting kamar yadda yake a wannan hoto na kasaSai Ku shiga Setting zai zai nuna muku haka kamar yadda yake a wannan photoSai ku danna wajen da nayi nuni wato Account kuna danna wa zai nuna muku yadda yake a wannan hoto na kasa


Ku shiga wajen nan da nayi nuni wato Two-step verification

Kana danna wa zai zo nan yadda yake a wannan hoto na kasa


A wannan fili zaku saka lambobi guda 6 ne sai ku danna next zai kai ku wajen saka email kamar hakaA nan sai ku saka email address din ku idan kuna bukata

Afanin email din shi ne idan kuka manta security din da kuka saka zasu tambaye ku email din kuna saka wa zasu turo muku lambobin ta email din

Idan kuma bakwa bukatar email din sai ku danna Skype ku wuce wajen ku danna confirm

Zai nuna muku hakaKu danna Done shikenan.

Idan kuma kuna son cirewa sai kubi wannan hanya

Duba hoton nan na kasa


Idan kuna son cire wa sai ku danna Disabled yadda yake a wanna hoto

Idan kuna son canza PIN din ma ga wajen nan a tsakiya idan kuma kuna son canza email Ku shiga layi na uku


Amfanin wannan security duk Wanda  yayi kokarin kutse cikin account din ka zasu tambaye ka lambobin.

Zamu dakata a nan sai kuma lokaci na gaba

Kuyi share zuwa Social media domin wadansu su amfana.

Thé M Jáméél


Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.