Monday, October 14, 2019
Shin gaskiya ne A'isha Buhari tayi yaji?

Home Shin gaskiya ne A'isha Buhari tayi yaji?

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
A kwanakin nan ne dai kafafen sada zumunta suka cika da jita jitar cewar Shugaba Muhammadu Buhari zai kara aure da kuma cewar uwar gidan sa wato A'isha Buhari ta yi yaji.

Source: voahausa.com


Hajiya Aisha Buhari, da ta kwashe kusan watanni biyu ba a ji duriyarta ba a Najeriya ta koma gida yau Lahadi daga kasar Birtaniyya. A lokacin da ta isa tashar jiragen saman birnin tarayya Abuja ‘yan jarida sun yi ma ta ca da tambayoyi akan abin da ke faruwa.
Hajiya Aisha ta bayyana cewa ta je ganin ‘yayanta ne a Birtaniyya, abinda kamar wata al’ada ce a garesu ta zuwa hutu a lokacin da suka sami dama. Ta kuma ce ta sami damar a duba lafiyar ta a London saboda ba ta ji dadin jikinta ba.
Da take maida martani game da jita jitar cewa shugaba Muhammadu Buhari zai auri Ministar ayyukan jinkan Najeriya Hajiya Sadiya Umar Farouq, Hajiya Aisha ta ce ba ta da masaniya akan abinda ya faru tun da ba ta nan, amma wanda aka ce zai yi auren ne ya kamata ya yi bayani.
“Amma ita wadda aka ce za a aura, wanda ya gaya mata za a aure ta, ba ta yi zaton ba a daura auren ba, don sai da ta ji shiru ba labari sannan ta fito ta musanta batun,” a cewar Hajiya Aisha.
Game da batun yajin da aka ce ta yi, uwar gidan shugaban ta ce tun da aka ce mai gidanta (Shugaba Muhammadu Buhari) ya mutu lokacin da ya je London jinya to ba jita jitar da jama’a ba zasu iya yadawa ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.