Wednesday, October 23, 2019
Rashin mijin aure ne ya kawo mun tsaiko Maryam Yahaya

Home Rashin mijin aure ne ya kawo mun tsaiko Maryam Yahaya

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Shahararriyar jarumar Kannywood, Marayam Yahaya ta bayyana dalilin da yasa bata yi aure ba har yanzu.


A cewar jarumar rashin mijin aure ne ya kawo mata wannan tsaikon

A kwanakin baya ne Abubakar Bashir Maishadda ya bayyana cewa, Allah ne bai yi auren sa da jarumar ba"

Jarumar ta bayyana hakan ne a hirar da tayi da gidan rediyon Freedom dake Kano. Jarumar tace: "Da aure da mutuwa duk lokaci ne, idan lokaci kuwa yayi ai zan daga. Baabu mijin ne, hakan ne ya hanani auren. Ku fito ku aureni, kunsan aure maza yanzu wuya suke.

A kwankin baya ne dai hotuna suka dinga yawo a kafafen sada zumunta ana cewa, an kasa Maryam Yahaya don kuwa saurayinta Maishadda zai angwance da matashiyar jaruma Hassana Muhammad. Sai dai, a wata hirar da gidan rediyon Freedom yayi da Abubakar Bashir Maishadda, ya tabbatarwa da gidan rediyon cewa tabbas ya taba soyayya da Maryam. Amma Allah ne bai nufa zai aureta ba domin yanzu haka an kusa bikinsa. Shararriyar jarumar na daga cikin manyan jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a masana'antar ta Kannywood.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.