Tuesday, September 24, 2019
Yadda zaka sauke Video ko Mp3 daga YouTube

Home Yadda zaka sauke Video ko Mp3 daga YouTube

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Maziyarta shafin mu na ZaurenHausa barkan ku da sake saduwa da mu a daidai wannan lokaci
A yau zamu yi bayani ne game da hanya mai sauki da zaka bi domin sauke video ko mp3 kai tsaye daga YouTube,

Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen sauke video daga shafin YouTube amma ina ganin wannan ita ce hanya mafi sauki wanda kuma har ma zaka iya sauke abun da kake bukatar a matsayin Mp3 (Audio),

Da farko zaka sauke wani application mai suna kamar haka VidMate domin sauke wannan application zaka iya ziyartar Apkpure.com ko kuma kai tsaye ka yi search a browser din ka kamar haka

Download VideMate old version kai tsaye zaka samu link da zai kai ka zuwa inda zaka sauke shi a kan wayar ka ka yi Install din sa
Dalilin da yasa ban ce ku sauke a Play store ba shi ne sabo da New Version ne kawai zaku samu a can a inda kuma old version ne ake bukata,

Bayan ka bude VideMate application ka duba can saman sa akwai box na search ka rubuta sunan video da kake bukata zasu bayyana kamar yadda yake a wannan hoto dake kasa
To abun da zaka yi shi ne sai ka dannan Download zai kawo ka yadda yake a wannan hoto dake kasa
To a nan kamar yadda kuke gani sun bayar da zabi idan video din ne sai ka zabi size da kake bukata idan kuma mp3 kake bukata gashi nan sai ka zaba ka sauke.


A nan muka kawo karshen wannan bayani

Kuci gaba da bibiyar ZaurenHausa

Ku yi share zuwa social media domin wadansu su amfana

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.