Sunday, September 22, 2019
Hanyoyin da zaka bi domin gane takardar kudi ta jabu

Home Hanyoyin da zaka bi domin gane takardar kudi ta jabu

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Akwai mutane da yawa da suka fada hannun mazambata sabo da basa iya tantance takardar kudi ta kwarai da ta jabu wanda dalilin hakan suka tafka hasara wannan dalili ne ya sa a yau zamu kawo muku wadansu hanyoyi da masana suka fito da su game da yadda zaka iya banbance kudin jabu wato (Fake Money)

Ku biyo mu,

1> Shafa
Hanya ta farko da zaka gane takardar kudi ta jabu shi ne rike wa a hannu ka shafa idan ka ji ta fiye laushi kamar takarda to kudin jabu ne kada ka karba..,

2>Ruwa
Hanya ta biyu da zaka gane kudin jabu shi ne ka jika hannun ka da ruwa sannan ka shafi takardar kidin idan kaga kalar su ta fara wanke wa to kada ka karba na jabu ne
Haka ma zaka iya samun ruwa ka saka kudin a ciki kimanin sakan 30 da zaran kaga launin kudin ya fara canza ruwan to hakan na nufin jabu ne..,

3>Hatimi
Hanya ta uku da zaka gane takardar kudi ta jabu shi ne akwai wani hatimi a jikin Naira 1000 mai launin gwal to idan jabun kudi ne ka gwada kankare wannan hatimi da hannun ka zaka ga ya wuce..,

4>Zare
Hanya ta hudu da zaka iya gane jabun kudi shi ne ko wane takardar kudi akwai wani zare mai sheki yana da tsayi dai dai da takardar kudin yana da dan kauri yadda hannu zai iya jin sa ya fi bayyana a tsofoffin takardun kudi to idan jabun kudi ne zaka ga zaren bashi da kauri sosai kamar na kudin kwarai sannan yana da saurin kankaruwa da zaka gwada..,

5>Haske
Hanya ta biyar da zaka iya gane jabun kudi shi ne amfani da kwan lantarki mai dauke da sinadarin MERCURY akwai wasu abubuwa jikin takardar kudi da ido baya iya ganin su ba tare da taimakon hasken wutar lantarki mai dauke da MERCURY ba wanda ko wacce takardar Naira na dauke da su
Idan kayi amfani da wannan hanya ka duba takardar Naira 1000 da kwan wutar lantarki zaka ga an rubuta 1,000 da lambobi kwance a jikin takardar wanda idan kudin jabu ne zai ga abun a juye ne (UPSIDE DOWN).

Akwai hanyoyi da dama da ake gane jabun kudi amma wannan su ne masu sauki wadanda kowa ma zai iya.

Zamu dakata a nan sai kuma lokaci na gaba

Kuci gaba da kasancewa da Zaurenhausa.com

Sannan kuyi share zuwa yan uwa da abokan arziki domin su amfana.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.