Sunday, September 29, 2019
[Bollywood] Me kuka sani game da Amrish Puri

Home [Bollywood] Me kuka sani game da Amrish Puri

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Me kuka sani game da Amrish Puri [Mugyambo,]


Kusan dai kamar yadda kowa ya sani jarumi "AMRISH PURI" babbar inkiyar sa wacce yayi Suhura da ita ta fannin suna a duniyar fim a nan kasar hausa itace : "MUGYAMBO",
Ga dukkan wadanda suka kasance suna bibiyar fina-finan sa sun san cewa Jarumi AMRISH PURI ko kuma ince MUGYAMBO yayi matukar kaiwa kololowa wajen iya shirya TUGGU da MAKIDA da DASISA, haka zalika ya goge sosai wajen iya shirya HIYANA da dukkan wata kitimurmura,


Baya ga haka kuma shi din shaharren mugu ne kuma azzalumi ajin farko, amma fa duk acikin duniyar fim (ba wai a duniyar azahiriyya ba),
A fagen iya acting kuwa da isar da sako yadda mai kallo zai gamsu ainun-ainun, to fah magana ta gaskiya ni dai kam a wuri na sam-sam har wa yau bashi da madadi,
Domin kuwa kusan dukkanin kafatanin rubunan fina-finan sa babu na yarwa, matukar ka ganshi acikin fim to ka kalla kawai, domin baya hawa fim marar ma'ana,

Na kalli tarin tulin fina-finan sa masu yawan gaske, fim dinsa na farko da na fara kalla shi ne fim din "GHAYAL", na kalli fim din shekaru kusan 21 da suka shu'de ranar lahadi da misalin karfe 11:15
Daga nan kuma sai irinsu

- GATAK,
- SALAAKHEN,
- JEET,
- KOYLA,
- LOHA,
- DAMINI,
- DILWALE DIL HANIYALE JAYENGE
- BADAL, etc,

Nasan cewa wanda duk ya kalli wadannan fina-finan dana lissafo lallai zai amintu da batutuwan da na zayyano game da wannan  Jarumin mai suna "AMRISH PURI" wato MUGYAMBO,
Malam MUGYAMBO akwai kurari da muzurai da nuna isa da tumbatsa, da kuma barazana, amma fa idan akwai basawan a kusa dashi, idan kuwa basawa suka kare to fah baya kasala wajen arar kafar Kare matsera.


Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.