Saturday, July 6, 2019
Mata 6 mafiya shahara a Kannywood

Home Mata 6 mafiya shahara a Kannywood

Thé M Jáméél

Ku Tura A Social Media
Kyawawan jaruman Kannywood guda shida,


Kamfanin fim na Kannywood ya sami albarka tare da kwararrun mata masu ban sha'awa da kuma basirar da suka dace da su.

Wadannan 'yan mata ba kawai suna da kyau ba amma suna aiki tukuru ,

RAHAMA SADAU
Rahama Sadau matashiyar jaruma ce mai hankali an haife ta a jihar Kaduna a ranar 7 ga Dismember Shekarar 1993, tana da digiri a harkar kasuwanci ta kasance daya daga cikin shahararrun 'yan wasan Kannywood bayan fim din ta da ake kira Gani Ga Wane Rahama Sadau tana da burin zama shahararriyar yar wasa kuma ta cimma burin ta,

HADIZA GABON
Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon tana daga cikin manyan yan wasan Kannywood kuma kyakkyawa ce matuka an haifeta a ranar 1 ga watan yuni a 1989 a garin Libreville a kasar Gabon ta fito cikin fim din Ali Yaga Ali,

NAFISAT ABDULLAHI
Nafisa Abdullahi yarinya ce kyakkyawa cikin yan mata na Kannywood kuma kwararriyar yar wasa an haifeta a garin Jos na jihar Filato ranar 23 ga watan Janairu shekarar 1990 Allah ya arzuta nafisa da fata mai kyau ta taka rawar gani cikin fim din Sai Wata Rana,

FATIMA ABDULLAHI
Jarumar da aka fi sani da Fati Washa ita ma kyakkyawa ce mai ban sha'awa kwarai da gaske an haifeta ranar 21 ga watan Faibrairun 1993,

UMMI IBRAHIM
Ummi Ibrahim da aka fi sanin ta da Zeezee jaruma ce kuma mai kudi da ta taka rawar gani a masana'antar ta Kannywood ta kasance cikin yan mata mafiya shahara a masana'antar masoyiya ce ga mawakin nan na kudu wato Timaya,

HAFSAT IDRIS
Hafsat da aka fi sani da Hafsat Barauniya ita ma tana daga cikin shahararrun mata a masana'antar Kannywood an haifeta a garin Shagamu ta fito cikin Fina-Finai daban daban ciki har da shahararren Fim din ta na Barauniya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments:

Note: Only a member of this blog may post a comment.