Sunday, November 24, 2019

RIKICI A KANNYWOOD LAIFIN NI DA ALI NUHU NE ADAM A ZANGO

RIKICI A KANNYWOOD LAIFIN NI DA ALI NUHU NE ADAM A ZANGO

Shahararren jarumi a masana'antar Fim ta Kannywood Adamu Abdullahi Zango wato (Adam A Zango) ya ce yaran sa da yaran Ali Nuhu sune ke haifar da matsala da rashin jituwa a Kannywood din.

Jarumi Adamu Zango ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Radio France International wato RFI.


Cikin wata tattaunawa da jarumin yayi da gidan Radio France International (RFI) ya bayyana cewa rikici da matsalolin da yaran sa dana fitaccen jarumi Ali Nuhu ke haifarwa a Kannywood ba laifin kowa ba ne sai shi da jarumi Ali Nuhu.

A cewar Adamu Zango da ace suna tsawatarwa ga yaran nasu to da zasu iya dakatar da su daga yin duk wani abu da zai haifar da rikici a masana’antar.

Jarumi Adam Zango ya kara da cewa ta bangarensa bai yadda yaransa su ci zarafin wani jarumi ba.

Idan zaku iya tunawa dai a watannin baya ne wani rikici ya kunno kai tsakanin manyan jaruman guda biyu wanda har sai da ta kai ga anje kotu, inda daga bisani kuma aka samu yin sulhu a tsakanin su.

Saturday, November 23, 2019

DAFA SHAYI NE GADO NA BA WAKA BA ADO GWANJA

DAFA SHAYI NE GADO NA BA WAKA BA ADO GWANJA

Jarumi a masana'antar Fim ta Kannywood kuma shahararren mawakin Hausa Ado Isa Gwanja ya ce ko kusa shi ba dan daudu ba ne.

Silar fitowa ta a matsayin dan daudu a Fim shi ne akwai wani Fim da aka bukaci dan daudu ciki aka nemi 'yan daudu jar su 50 cikin su aka rasa wanda zai iya shi ne sai aka ce bara to a gwada dan masana'antar ana gwadani kuwa na yi dace da wurin,

Wannan shi ne farkon fara fitowa ta a dan daudu inji Ado Gwanja,

Farko dai Ado Gwanja ya fara ne da rera wakoki kasancewar bai samu karbuwa ba sai ya juya akalar sa zuwa fito wa a Fim

Wakokin Gwanja dai sun fi karbuwa ne wajen mata kamar yadda zaka ji a mafiya yawan wakokin sa mata yafi ambata ymawakin ya ce yana yin haka ne sabo da su mata sun fi son biki ma'abota nishadi ne
To wa zan ambata idan ba mata ba?" A cewar sa.

Gwanja ya musanta zargin da ake yi masa cewa yana furta kalmomin batsa cikin wakokin sa a inda yace To ni dai da Hausa nake waka kuma bahaushe yana da fahimta a iya sani na a duk wakoki na ba abun da ya shafi batsa ko kusa,


Matashin ya fara waka ne kusan shekaru 10 da suka gabata
Ra'ayi ne ya sa na fara waka" a cewar sa.

Ya kara da cewa shi ba gadon waka yayi ba shige yayi sai Allah ya bashi baiwa har ya samu karbuwar da yake kai a halin yanzu,

Yace idan gado ne da dafa shayi zan gada domin shi ne sana'ar mahaifi na a Kano"Kamar yadda yake a bayyane cewa mafi yawan jarumai ko mawaka na cin karo da matsaloli, sai dai Gwanja ya ce duk wanda ya samu kansa a matsala "to shi ya ga dama ya shige ta."
Kazalika mawakin ya ce shi a saninsa ba shi da wasu makiya ko abokan adawa a wannan harka, idan ma kuma akwai su to bai san da su ba. "Kazantar da ba ka gani ba kuma tsafta ce," in ji shi.


Friday, November 22, 2019

9MOBILE YADDA ZAKA SAYI 1GB A KAN KUDI NAIRA 200

9MOBILE YADDA ZAKA SAYI 1GB A KAN KUDI NAIRA 200

Wannan dai ba sabon abu ba ne ga masu amfani da layin Etisalat wato 9MOBILE to sai dai zamu maimaita ne kasancewar ba kowa ne yake da masaniya a kai ba.

Sabo da haka ne zamu sake magana a kai

Masu amfani da layin etisalat sun dade suna morar wannan Data mai saukin farashi,

Ba tare da bata lokaci ba ga hanyar da zaka bi domin siyen 1gb wato 1000mb a kan kudu NAIRA 200 Kacal.


Farko ka saka katin Naira 200 a layin ka na 9Mobile #ETISALAT.

Sai ka danna wadannan lambobi

*929*10#.

Nan take zasu kwashe kudin su baka damen shiga yanar gizo 1000MB na tsawan kwanaki 3.


Kuma dadin abun wannan data komai zaka iya yi da ita kama daga

Facebook

WhatsApp

Instagram

Twitter

Telegram

YouTube


Da dai sauransu


Zamu dakata a nan.


Kuci gaba da bibiyar ZaurenHausa a ko da yaushe.


Kuyi share zuwa Social media domin wadansu su amfana.


Thursday, November 21, 2019

RUKAYYA DAWAYYA A YANZU BANI DA SAURAYI A KANNYWOOD

RUKAYYA DAWAYYA A YANZU BANI DA SAURAYI A KANNYWOOD

A YANZU BANI DA SAURAYI a Kannywood cewar rukayya dawayya
Cikin shirin daga bakin mai ita da #BBC HAUSA suka kaddamar a yau sun yi hira ne da shahararriyar jaruma a masana'antar Kannywood wacce taga jiya taga yau wato Rukayya Umar wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya.

Ga kadan daga cikin tambayoyin da aka yi mata da kuma amsoshin da ta bayar,


1 Wanene saurayin ki a Kannywood?

Rukayya. "A yanzu bani da saurayi a Kannywood"

2 Da wa koka taba yin soyayya a Kannywood?

Rukayya. "Misbahu Ahmad"

3 Wanene saurayinki na farko?

Rukayya. Kasancewar ba a Nigeria na girma ba na girma ne a kasar Saudiyya saurayi na na farko wani balarabe ne sunan sa Faisal".

4 Yaushe zaki sake aure?

Rukayya. Nan ba da dade wa ba"

5 Me kike fara yi idan kika tashi daga barci?

Rukayya. Kasancewar gidana hana da fadi nakan fito na zagaya ina duba filawowi sai na zauna na yi ta Azkar"

6 Yaruka nawa kika iya magana da su?

Rukayya. Yaruka 3 Hausa Larabci Fulatanci English.

Zamu dakata a nan sai wani lokaci na gaba.

Kuci gaba da bibiyar zaurenhausa a ko da yaushe.

Sunday, November 3, 2019

Yadda Zaka Sauke Free Template A Blogger

Yadda Zaka Sauke Free Template A Blogger

A yau zan yi takaitaccen bayani game da yadda zaka sauke free template a shafin ka na Blogger.

Ba tare da bata lokaci ba ga yadda zaka dora Template a Blogger

Farko ka bude blogger.com

Bayan ya bude sai ka zabi Theme kamar yadda yake a wannan hoto

Bayan ya bude sai ka duba sama bangaren hannun dama ka danna wajen da kibiya ta yi nuni a wannan hoto dake kasa

Bayan ka danna Backup/Restore zai bude kamar haka sai ka danna wajen da kibiya ta yi nuni

Bayan ka danna zai kawo ka nan

Ka danna wajen da kibiya ta yi nuni zai kawo ka nan


KARANTA DARASI MAI ALAKA DA WANNAN Yadda Zaka Gyara Free Template


Ka danna wajen da kibiya ta yi nuni zai kawo ka nan

Zaka ga Template da ka sauke karshen sa .XML shi zaka dora.


Yadda Zaka Gyara Free Template

Yadda Zaka Gyara Free Template

Duba da yadda naga wadansun mu suna tambaya game da yadda ake gyara free template domin sauke shi a Blogger hakan ya sa zan yi bayani a kai.


Kamar dai yadda kusan kowa ya sani akwai shafukan sayar da template kuma suna bayar da na kyauta to sai dai ba kowa ne ya iya gyara wa bayan ya sauke ba,


Ga cikakken bayani game da yadda zaka gyara free template bayan ka sauke shi..

Farko dai akwai bukayar ka sauke Application mai suna Ex file explore

Bayan ka sauke sai ka bude shi kamar haka

Sai ka zabi storage na wayar ka ka danna zai bude kamar haka

Kasncewar Download ka yi sai ka dannawajen da Arrow ta yi nuni zai bude kamar haka

Idan ka duba zaka ga sunan template din da ka sauke karshen sa da .zip sai ka danne shi ya yi mack bayan yayi mack sai ka duba kasa hannun dama ka Danna More gashi nan a hoton can na sama

Bayan ka Danna more zai bude kamar haka

Sai ka danna Extract To kamar yadda Arrow yayi nuni bayan ka danna zai bude kamar haka


Sai ka danna Ok

Ka gama gyaran Free template

A darasi na gaba zan yi bayani game da yadda zaka dora shi a shafin ka na Blogger.

Friday, November 1, 2019

Yadda Jarumi Ali Nuhu Ya Samu Karramawa A Kasar Indiya

Yadda Jarumi Ali Nuhu Ya Samu Karramawa A Kasar Indiya

A makon da ya gabata ne dai Jarumin masana'antar Fim ta Kannywood wato Ali Nuhu ya samu karramawa a kasar Indiya.

Ya samu karramawar ne daga wadansu dalibai 'yan Arewacin Nigeria da kuma malaman su Indiyawa a kasar ta Indiya bayan sun gayyace shi wani taron Al'adu

Daliban na karanta fannoni daban-daban kama daga fannin likita zuwa hada magunguna da injiniya da sauransu,” in ji Ali Nuhu kamar yadda ya shaida wa BBC. Jarumin ya ce baya ga wadannan dalibai, wasu makarantu a kasar sun ba shi lambobin yabo.

KARANTA WANNAN. Juruman 'Yan Mata 6 Mafiya Shahara A Kannywood

Ali Nuhu ya ce “Akwai makarantar Dayananda Sagar School of Physiotherapy su ma sun ba ni lambar yabo kuma sun nuna jin dadinsu kan yadda daliban Najeriya ke mayar da hankali kan karatunsu.”

Jarumin ya ce ya yi matukar farin ciki da wannan karramawa da kuma yadda malaman wadannan makarantu ke da sha’awar al’adun Hausawa. “Wadansu daga cikin malaman har fina-finan Hausa suke kallo saboda su ga yadda yanayin rayuwar Bahaushe take.

“Shi ya sa idan wani dan wasa ya zo taro irin wannan sukan karrama shi,” inji Ali Nuhu.


Wednesday, October 30, 2019

[[Karanta]] A gaskiya ni ban iya Hausa ba Zahra Buhari

[[Karanta]] A gaskiya ni ban iya Hausa ba Zahra Buhari

'Yar Shugaban kasa Zahra Buhari ta bayyana cewa ita fa bata iya magana da harshen Hausa sosai ba.

Zahra Muhammadu Buhari ta bayyana hakan ne a yayin wani taro da gidan Radion BBC ya shirya domin wadanda suka lashe gasar gasar da suke gabatar wa mai tajen 'HIKAYATA' wanda suka saba shirya wa ko wace shekara a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja,
Mahaifin Zahra wato Shugaba Muhammad Buhari dai kamar yadda kowa ya sani Bafullatani ne garin Daura na jihar Katsina haka ma mahaifiyar ta matar shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ita ma Bafullatana ce daga jihar Adamawa,

Zan baku mamaki domin bazan iya magana da hausa ba domin ko a gida idan ina magana da Hausa baban mu dariya yake yi mun inji Zahra"


Ta cigaba da cewa “Munyi rayuwar makaranta ne da fararen fata sannan kuma muna hada Hausa da turanci ne idan muna magana a gida” A karshe ta bayyana cewa yawanci a gida suna magana ne da fulatanci Wanda hakan yasa Hausa take yi mata wahala.

Monday, October 28, 2019

Akshay Kumar Fina Finan Sa 14 Mafiya Shahara

Akshay Kumar Fina Finan Sa 14 Mafiya Shahara

Jarumi Akshay Kumar yana daya daga cikin taurari a masana'antar Bollywood a yau zamu kawo muku wadansu cikin Faina-finan sa tare da shekaraun fitar su.

Ku biyo ni.

1: Saugandh, Ya fita a shekarar (1991)

2: Khiladi, Ya fita a shekarar (1992)

3: Waqt hamara hai, Ya fita a shekarar (1993)

4: Sainik, Ya fita a shekarar (1993)

5: Yeah dillagi, Ya fita a shekarar (1994)

6: . Main Khiladi Tu Anari. Ya fita a shekarar (1994)

7:  Mohra, Ya fita a shekarar (1994)

8: Sabse Bada Khiladi, Ya fita a shekarar (1995)

9:  Khiladiyon Ka Khiladi, Ya fita a shekarar (1996)

10: Dil To Pagal Hai, Ya fita a shekarar (1997)

11: Mr. & Mrs. Khiladi, Ya fita a shekarar (1997)

12: Sangharsh, Ya fita a shekarar (1999)

13: Jaanwar, Ya fita a shekarar (1999)


14: Hera Pheri, Ya fita a shekarar (2000)

Akshay Kumar yana da daruruwan shahararrun fina finai amma duk da haka zamu dakata a nan sai kun sake jin mu a karo na gaba.

Saturday, October 26, 2019

Friday, October 25, 2019

Auren Sharukh Khan Da Gauri ya cika shekaru 28

Auren Sharukh Khan Da Gauri ya cika shekaru 28

A rana mai kamar ta yau ne 25 ga Satan October auren fitattun jaruman nan na masana'antar Bollywood wato Sharukh Khan da matar sa Gauri Khan ya cika shekaru 28 cif,


An daura auren ne 25 ga watan October shekarar 1991,


Har yanzu dai masoyan biyu suna zaman su cikin koshin lafiya a matsayin ma'aurata a inda Allah ya arzuta su da 'ya'ya 3 a tsawon wadannan shekaru.

'Ya'yan nasu su ne Aryan Khan,
Suhana Khan, AbRam Khan,

A wannan karo ma masoyan sun shirya kayataccen biki tare da gayyatar 'yan uwa da abokan arziki da masoya,

Ma'auratan 2 Sharukh Khan wanda mabiyin Addinin Musulunci ne da matar sa Gauri Khan wacce ke bin Addinin Buddha sunan so ba zai taba mantuwa ba a Bollywood.

Wednesday, October 23, 2019

Rashin mijin aure ne ya kawo mun tsaiko Maryam Yahaya

Rashin mijin aure ne ya kawo mun tsaiko Maryam Yahaya

Shahararriyar jarumar Kannywood, Marayam Yahaya ta bayyana dalilin da yasa bata yi aure ba har yanzu.


A cewar jarumar rashin mijin aure ne ya kawo mata wannan tsaikon

A kwanakin baya ne Abubakar Bashir Maishadda ya bayyana cewa, Allah ne bai yi auren sa da jarumar ba"

Jarumar ta bayyana hakan ne a hirar da tayi da gidan rediyon Freedom dake Kano. Jarumar tace: "Da aure da mutuwa duk lokaci ne, idan lokaci kuwa yayi ai zan daga. Baabu mijin ne, hakan ne ya hanani auren. Ku fito ku aureni, kunsan aure maza yanzu wuya suke.

A kwankin baya ne dai hotuna suka dinga yawo a kafafen sada zumunta ana cewa, an kasa Maryam Yahaya don kuwa saurayinta Maishadda zai angwance da matashiyar jaruma Hassana Muhammad. Sai dai, a wata hirar da gidan rediyon Freedom yayi da Abubakar Bashir Maishadda, ya tabbatarwa da gidan rediyon cewa tabbas ya taba soyayya da Maryam. Amma Allah ne bai nufa zai aureta ba domin yanzu haka an kusa bikinsa. Shararriyar jarumar na daga cikin manyan jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a masana'antar ta Kannywood.

Thursday, October 17, 2019

Postal Code na jihohin Nigeria

Postal Code na jihohin Nigeria

A yau zamu kawo muku jerangiyar Postal Codes na jihohin Nigeria domin amfanin yan uwa masu bukata, duk da zamu iya cewa kusan kowa ma yana da bukatar sa

Menene Postal Code?


A takaice dai Postal Code shi ne wadansu lambobi guda 6 da ko wacce jiha a ko wace nahiya da kuma ko wace kasa tana da su wanda a takaice amfanin su shi ne idan zaka yi register da wadansu kamfanunuwa na kasashen waje ko ma wadansu cikin kasar ka bayan cikakken suna da wadansu bayanai zasu iya bukatar Postal Code din ka

Yana daga cikin amfanin #Postal Code a duk lokacin da ka sayi kayayyaki a intanet musamman daga kasashen waje to zasu bukaci Postal Code din ka ne domin turo da kayan zuwa Post Office na jihar ka kaje ka karba,

A takaice kenan amfanin Postal Code

Ga jerangiyar Postal Codes na jihohin Nigeria.

Abuja  postal code            900001

Abia  postal code       440001

Adamawa  postal code    640001

Akwa-Ibom  postal code  520001

Anambra  postal code    420001

Bauchi  postal code     740001

Borno  postal code      600001

Delta  postal code      320001

Edo  postal code        300001

Enugu  postal code      400001

Imo  postal code        460001

jigawa  postal code     720001

Kano  postal code       700001

Kaduna  postal code     800001

Katsina  postal code    820001

Kebbi  postal code      860001

Kogi  postal code       260001

Kwara  postal code      240001

Lagos  postal code   100001

Niger  postal code      920001

Ogun  postal code       110001

Ondo  postal code       340001

Osun  postal code       230001

Oyo  postal code        200001

Plateau  postal code    930001

Rivers  postal code     500001

Sokoto  postal code     840001

Taraba  postal code     660001

Yobe  postal code       320001

Ebonyi  postal code     840001

Kuyi share zuwa 'yan uwa da abokan arziki domin kowa ya amfana

Monday, October 14, 2019

Shin gaskiya ne A'isha Buhari tayi yaji?

Shin gaskiya ne A'isha Buhari tayi yaji?

A kwanakin nan ne dai kafafen sada zumunta suka cika da jita jitar cewar Shugaba Muhammadu Buhari zai kara aure da kuma cewar uwar gidan sa wato A'isha Buhari ta yi yaji.

Source: voahausa.com


Hajiya Aisha Buhari, da ta kwashe kusan watanni biyu ba a ji duriyarta ba a Najeriya ta koma gida yau Lahadi daga kasar Birtaniyya. A lokacin da ta isa tashar jiragen saman birnin tarayya Abuja ‘yan jarida sun yi ma ta ca da tambayoyi akan abin da ke faruwa.
Hajiya Aisha ta bayyana cewa ta je ganin ‘yayanta ne a Birtaniyya, abinda kamar wata al’ada ce a garesu ta zuwa hutu a lokacin da suka sami dama. Ta kuma ce ta sami damar a duba lafiyar ta a London saboda ba ta ji dadin jikinta ba.
Da take maida martani game da jita jitar cewa shugaba Muhammadu Buhari zai auri Ministar ayyukan jinkan Najeriya Hajiya Sadiya Umar Farouq, Hajiya Aisha ta ce ba ta da masaniya akan abinda ya faru tun da ba ta nan, amma wanda aka ce zai yi auren ne ya kamata ya yi bayani.
“Amma ita wadda aka ce za a aura, wanda ya gaya mata za a aure ta, ba ta yi zaton ba a daura auren ba, don sai da ta ji shiru ba labari sannan ta fito ta musanta batun,” a cewar Hajiya Aisha.
Game da batun yajin da aka ce ta yi, uwar gidan shugaban ta ce tun da aka ce mai gidanta (Shugaba Muhammadu Buhari) ya mutu lokacin da ya je London jinya to ba jita jitar da jama’a ba zasu iya yadawa ba.

Sunday, October 6, 2019

Yadda zaka tsare WhatsApp din ka daga masu kutse

Yadda zaka tsare WhatsApp din ka daga masu kutse

Masu bibiyar ZaurenHausa barkan mu da wannan lokaci
A yau zamu yi bayani ne game da yadda zaku tsare akawun din ku na WhatsApp daga sharrin masu kutse.


A yanzu halin da ake ciki wadansu bata garin mutane sun fito da wani salo na kwace wa mutane WhatsApp din su ba tare da sun sani ba,

Wadannan bata garin mutane zasu iya hawa WhatsApp din ka a duk lokacin da suka ga dama ba tare da ka sani ba a inda zasu iya amfani da wannan dama wajen aiwatar da duk abun da suke bukata ko dai su damfari wadansu ko wani abu daban,

Wannan dalili ne yasa muka zo muku da hanyar da zaku bi domin tsare naku akawun din daga sharrin su

Ku biyo ni


Farko idan ka bude WhatsApp application din ka ka duba can sama hannun dama sai Ku danna wannan digo 3 kamar yadda yake a wannan hoto dake kasaBayan kun danna zai baku option ciki har da Setting kamar yadda yake a wannan hoto na kasaSai Ku shiga Setting zai zai nuna muku haka kamar yadda yake a wannan photoSai ku danna wajen da nayi nuni wato Account kuna danna wa zai nuna muku yadda yake a wannan hoto na kasa


Ku shiga wajen nan da nayi nuni wato Two-step verification

Kana danna wa zai zo nan yadda yake a wannan hoto na kasa


A wannan fili zaku saka lambobi guda 6 ne sai ku danna next zai kai ku wajen saka email kamar hakaA nan sai ku saka email address din ku idan kuna bukata

Afanin email din shi ne idan kuka manta security din da kuka saka zasu tambaye ku email din kuna saka wa zasu turo muku lambobin ta email din

Idan kuma bakwa bukatar email din sai ku danna Skype ku wuce wajen ku danna confirm

Zai nuna muku hakaKu danna Done shikenan.

Idan kuma kuna son cirewa sai kubi wannan hanya

Duba hoton nan na kasa


Idan kuna son cire wa sai ku danna Disabled yadda yake a wanna hoto

Idan kuna son canza PIN din ma ga wajen nan a tsakiya idan kuma kuna son canza email Ku shiga layi na uku


Amfanin wannan security duk Wanda  yayi kokarin kutse cikin account din ka zasu tambaye ka lambobin.

Zamu dakata a nan sai kuma lokaci na gaba

Kuyi share zuwa Social media domin wadansu su amfana.

Thé M Jáméél


Saturday, October 5, 2019

[MTN] Yadda zaka sayi 2gb a kan kudi Naira 500 kacal

[MTN] Yadda zaka sayi 2gb a kan kudi Naira 500 kacal

A yau muna tafe da wata garabasa ga masu amfani da layin sadarwa na MTN,


Ba tare da bata lokaci ba garabasar shi ne yadda zaku sayi damen shiga yanar gizo wato [DATA]
Zaku iya siyen MB 2000 wato 2gb a kan kudi Naira dari biyar kacal a layukan ku na MTN,


Ga yadda zaku yi domin siya

Bayan kun tabbatar kun zaka katin 500 a layin ku sai ku danna wadannan lambobi
*131*154#
Nan take zasu kwashe 500 su baku 2gb wanda zai yi tsawon kwanaki 3 kuna amfani da shi zaku iya shiga ko ina a yanar gizo da shi.


Zamu dakata a nan sai kuma lokaci na gaba.

Tuesday, October 1, 2019

Sunday, September 29, 2019

[Bollywood]  Me kuka sani game da Amrish Puri

[Bollywood] Me kuka sani game da Amrish Puri

Me kuka sani game da Amrish Puri [Mugyambo,]


Kusan dai kamar yadda kowa ya sani jarumi "AMRISH PURI" babbar inkiyar sa wacce yayi Suhura da ita ta fannin suna a duniyar fim a nan kasar hausa itace : "MUGYAMBO",
Ga dukkan wadanda suka kasance suna bibiyar fina-finan sa sun san cewa Jarumi AMRISH PURI ko kuma ince MUGYAMBO yayi matukar kaiwa kololowa wajen iya shirya TUGGU da MAKIDA da DASISA, haka zalika ya goge sosai wajen iya shirya HIYANA da dukkan wata kitimurmura,


Baya ga haka kuma shi din shaharren mugu ne kuma azzalumi ajin farko, amma fa duk acikin duniyar fim (ba wai a duniyar azahiriyya ba),
A fagen iya acting kuwa da isar da sako yadda mai kallo zai gamsu ainun-ainun, to fah magana ta gaskiya ni dai kam a wuri na sam-sam har wa yau bashi da madadi,
Domin kuwa kusan dukkanin kafatanin rubunan fina-finan sa babu na yarwa, matukar ka ganshi acikin fim to ka kalla kawai, domin baya hawa fim marar ma'ana,

Na kalli tarin tulin fina-finan sa masu yawan gaske, fim dinsa na farko da na fara kalla shi ne fim din "GHAYAL", na kalli fim din shekaru kusan 21 da suka shu'de ranar lahadi da misalin karfe 11:15
Daga nan kuma sai irinsu

- GATAK,
- SALAAKHEN,
- JEET,
- KOYLA,
- LOHA,
- DAMINI,
- DILWALE DIL HANIYALE JAYENGE
- BADAL, etc,

Nasan cewa wanda duk ya kalli wadannan fina-finan dana lissafo lallai zai amintu da batutuwan da na zayyano game da wannan  Jarumin mai suna "AMRISH PURI" wato MUGYAMBO,
Malam MUGYAMBO akwai kurari da muzurai da nuna isa da tumbatsa, da kuma barazana, amma fa idan akwai basawan a kusa dashi, idan kuwa basawa suka kare to fah baya kasala wajen arar kafar Kare matsera.


Wednesday, September 25, 2019

Garabasa Yadda zaka sayi 1gb akan kudi Naira 300

Garabasa Yadda zaka sayi 1gb akan kudi Naira 300

Maziyarta shafin mu na Zaurenhausa barkan mu da wannan lokaci
Kamar yadda muka saba a yau ma mun zo muku da wata garabasa game da yadda zaku sayi damen shiga yanar gizo mai saukin kudi,

Kamar dai yadda kuka sani kwanaki mun kawo muku yadda ake siyen 1gb a kan kudi Naira 200 kacal a layin MTN to sai dai shi wancen din ba ko wane layi ke yi ba sannan suna dakatar da mutum ko wane lokaci..,


Sai dai shi wannan da muka zo muku da shi a yanzu yana yi a ko wane layi ba wata matsala'

Ba tare da bata lokaci ba

Farko ka saka Naira 300 a layin ka na MTN sannan ka danna wadannan lambobi *567*141# sai ka yi reply da 1 nan take zasu kwashe kudin su baka 1gb wato 1000mb wanda zaka yi amfani da shi tsawon kwanaki 7.

Zamu dakata a nan sai kuma lokaci na gaba

Kuci gaba da kasancewa da mu

Zaku iya share zuwa abokan ku ta hanyar WhatsApp Facebook Twitter domin su amfana.

Tuesday, September 24, 2019

Yadda zaka sauke Video ko Mp3 daga YouTube

Yadda zaka sauke Video ko Mp3 daga YouTube

Maziyarta shafin mu na ZaurenHausa barkan ku da sake saduwa da mu a daidai wannan lokaci
A yau zamu yi bayani ne game da hanya mai sauki da zaka bi domin sauke video ko mp3 kai tsaye daga YouTube,

Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen sauke video daga shafin YouTube amma ina ganin wannan ita ce hanya mafi sauki wanda kuma har ma zaka iya sauke abun da kake bukatar a matsayin Mp3 (Audio),

Da farko zaka sauke wani application mai suna kamar haka VidMate domin sauke wannan application zaka iya ziyartar Apkpure.com ko kuma kai tsaye ka yi search a browser din ka kamar haka

Download VideMate old version kai tsaye zaka samu link da zai kai ka zuwa inda zaka sauke shi a kan wayar ka ka yi Install din sa
Dalilin da yasa ban ce ku sauke a Play store ba shi ne sabo da New Version ne kawai zaku samu a can a inda kuma old version ne ake bukata,

Bayan ka bude VideMate application ka duba can saman sa akwai box na search ka rubuta sunan video da kake bukata zasu bayyana kamar yadda yake a wannan hoto dake kasa
To abun da zaka yi shi ne sai ka dannan Download zai kawo ka yadda yake a wannan hoto dake kasa
To a nan kamar yadda kuke gani sun bayar da zabi idan video din ne sai ka zabi size da kake bukata idan kuma mp3 kake bukata gashi nan sai ka zaba ka sauke.


A nan muka kawo karshen wannan bayani

Kuci gaba da bibiyar ZaurenHausa

Ku yi share zuwa social media domin wadansu su amfana

Sunday, September 22, 2019

Hanyoyin da zaka bi domin gane takardar kudi ta jabu

Hanyoyin da zaka bi domin gane takardar kudi ta jabu

Akwai mutane da yawa da suka fada hannun mazambata sabo da basa iya tantance takardar kudi ta kwarai da ta jabu wanda dalilin hakan suka tafka hasara wannan dalili ne ya sa a yau zamu kawo muku wadansu hanyoyi da masana suka fito da su game da yadda zaka iya banbance kudin jabu wato (Fake Money)

Ku biyo mu,

1> Shafa
Hanya ta farko da zaka gane takardar kudi ta jabu shi ne rike wa a hannu ka shafa idan ka ji ta fiye laushi kamar takarda to kudin jabu ne kada ka karba..,

2>Ruwa
Hanya ta biyu da zaka gane kudin jabu shi ne ka jika hannun ka da ruwa sannan ka shafi takardar kidin idan kaga kalar su ta fara wanke wa to kada ka karba na jabu ne
Haka ma zaka iya samun ruwa ka saka kudin a ciki kimanin sakan 30 da zaran kaga launin kudin ya fara canza ruwan to hakan na nufin jabu ne..,

3>Hatimi
Hanya ta uku da zaka gane takardar kudi ta jabu shi ne akwai wani hatimi a jikin Naira 1000 mai launin gwal to idan jabun kudi ne ka gwada kankare wannan hatimi da hannun ka zaka ga ya wuce..,

4>Zare
Hanya ta hudu da zaka iya gane jabun kudi shi ne ko wane takardar kudi akwai wani zare mai sheki yana da tsayi dai dai da takardar kudin yana da dan kauri yadda hannu zai iya jin sa ya fi bayyana a tsofoffin takardun kudi to idan jabun kudi ne zaka ga zaren bashi da kauri sosai kamar na kudin kwarai sannan yana da saurin kankaruwa da zaka gwada..,

5>Haske
Hanya ta biyar da zaka iya gane jabun kudi shi ne amfani da kwan lantarki mai dauke da sinadarin MERCURY akwai wasu abubuwa jikin takardar kudi da ido baya iya ganin su ba tare da taimakon hasken wutar lantarki mai dauke da MERCURY ba wanda ko wacce takardar Naira na dauke da su
Idan kayi amfani da wannan hanya ka duba takardar Naira 1000 da kwan wutar lantarki zaka ga an rubuta 1,000 da lambobi kwance a jikin takardar wanda idan kudin jabu ne zai ga abun a juye ne (UPSIDE DOWN).

Akwai hanyoyi da dama da ake gane jabun kudi amma wannan su ne masu sauki wadanda kowa ma zai iya.

Zamu dakata a nan sai kuma lokaci na gaba

Kuci gaba da kasancewa da Zaurenhausa.com

Sannan kuyi share zuwa yan uwa da abokan arziki domin su amfana.

Saturday, September 21, 2019